
Majalisar Dattijai ta amincewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aika da sojoji zuwa kasar Benin Republic.
Majalisar ta amince da tura sojojin dan samar da zaman lafiya a kasar da sauran kasashen Africa.
Hakan ya zo ne bayan da shugaba Tinubu ya aikewa da majalisar bukatar hakan.