Majalisar jihar Kaduna ta nemi a kama da hukunta tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da mukarrabansa saboda zargin lalata kudin jihar har Naira Biliyan 423.
Kwamiti na musamman da aka nada yayi binciken mulkin tsohon gwamnan bisa jagorancin dan majalisa Henry Zacharia ya kammala binciken da mikawa majalisar sakamakon abinda ya gani.
Kakakin majalisar, Yusuf Liman ya bayyana damuwa kan yanda yace ake zargin tsohon gwamnan da lalata Naira Biliyan 423.
Sannan ana zargin El-Rufai da kuma bayar da kwagila ba bisa ka’ida ba da satar dukiyar jama’a da kuma aikata ba daidai ba.
Rahoton kuma yace mafi yawancin kudaden da gwamnatin jihar ta ciwo bashi, ba’a yi amfani dasu yanda ya kamata ba.