Wasu ‘yan majalisar wakilai sun nemi cewa, a canja tsarin mulkin Najeriya da zai baiwa shugaban kasa damar yin mulki na shekaru 6 wa’di daya.
Sannan sun nemi a rika yin karba-karbar mulki tsakanin yankuna 6 da ake dasu a kasarnan.
Dan majalisar daga jihar Imo, Ikenga Ugochinyere ne ya bayyana hakan inda yace idan shugaban kasa, Gwamnoni suka rika yin wa’adi daya na shekaru 6 kawao, za’a samu saukin kashe kudi da kuma yin aiki me kyau.