Monday, April 14
Shadow

Da Duminsa: NNPP ta Dakatar da Sen. Kawu Sumaila, Ali Madakin Gini, Kabiru Alhassan Rurum da Abdullahi Sani Rogo daga jam’iyyar

YANZU-YANZU: NNPP A Kano Ta Dakatar Da Kawu Sumaila Da Rurum Da Ali Madaki

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu mambobinta, ciki har da sanata da ‘yan majalisar dokoki, bisa zargin aikata ayyukan da suka sabawa manufofin jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin.

Ya ce, daga cikin ‘yan majalisar da abin ya shafa akwai Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu, Alhaji Abdullahi Sani Rogo, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rogo, Alhassan Rurum mai wakiltar Rano/Kibiya, da kuma Ali Madakin Gini mai wakiltar mazabar Dala a majalisar wakilai.

Karanta Wannan  Kwamitin kula da sha'anin sojojin ruwa (Navy) na majalisar dokoki ta tarayya sun gana da hukumar Sojin ruwa domin binciko zargin yadda aka ci zarafin Seaman Abbas Haruna

Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa, jam’iyyar ta nuna rashin jin dadinta kan halayen wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya da aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar.

A cewarsa, duk da cewa jam’iyyar ta ba su tikitin takara kyauta a lokacin zabe, wasu daga cikinsu sun aikata abubuwan da su ka saba da manufofi, ka’idoji da kuma tsarin jam’iyyar.

MAJIYA: Daily Ngerian

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *