Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Amurka ta fara kawo makamai da zata yi amfani dasu wajan hare-haren da zata kai kan kungiyoyin ‘yan tà’àddà a Najeriya.
Masani kan harkar tsaro, Brant Philip ne ya bayyana haka inda yaje jiragen yaki dauke da makaman sun rika sauka a sansanin da Amurkar ta kafa a kasar Ghana wanda daga canne zata rika kawo harin.
Yace Amurkar ta shafe sati 2 kullun tana aiko jirgi mara matuki dan tattara bayanan sirri akan kungiyoyin na ÌŚWÀP da Bòkò Hàràm da sauransu.
