Rahotanni sun ce ‘yansanda sun yi harbi a iska a Tunga dake babbar birnin Jihar Naija watau Minna dan hana masu zanga-zanga tare babbar hanya.
Da farko dai ‘yansandan sun fara watsawa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa ne saidai daga baya masu zanga-zangar sun sake taruwa a waje daya.
Rahoton yace jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yansanda da sauransu sun cire duwatsu akan titi da matsa suka sa.