
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, ‘Yansanda sun kama ma’ikacin hukumar dake kula da babban birnin tarayya, Abuja FCTA me suna Mairiga Hassan Shaharu saboda zargin shine ya kwarmatawa ‘yan Jarida labarin cewa, Wike ya rabawa ‘ya’yansa filaye masu yawa a Abuja.
Rahoton yace an kamashine da yammacin ranar Talata kuma iyalansa basu san inda yake ba.
Rahoton yace akwai yiyuwar ana can ana azabtar dashi.
Mairiga Hassan Shaharu na aiki ne a bangaren dake kula da bayanan masu mallakar filaye a Abuja.
Rahoton yace wasu na kusa da Wike sun ce tun bayan da labarin cewa ya mallakawa ‘ya’yansa filaye ya bayyana, Wike ya haukace ya rika shan giya fiye da yanda yake sha a baya.
Rahoton yace sai zage-zage yake, har matarsa bata tsira ba sai zaginta yake saboda abin ya masa haushi.