
Rundunar ‘yansandan Najeriya a jihar Kano ta ce ta kama mutum 17 kan zarginsu da aikata daba da kuma shirya zanga-zanga.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce bayanan sirri da ta tattara ne suka ba ta nasarar kama mutanen, amma ba ta bayyana dalilin shirya zanga-zangar ba.
Sai dai bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa wasu matasa sun taru a kusa da gidan sarki na Nassarawa, wanda Sarkin Kano na 15 Aminu Ado ke ciki, kafin ‘yansanda su tsarwatsa su da safiyar yau Laraba.
“Bayan samun bayanan sirri game da shirin zanga-zangar tayar da fitina da wasu ke yi, ‘yansanda tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro sun fita wasu muhimman wurare a ƙwaryar birnin Kano domin daƙile zanga-zangar,” a cewar sanarwar.
Har yanzu batun masarautar Kano na ci gaba da jan hankalin mazauna jihar, inda Aminu Ado da Muhammadu Sanusi ke bayyana kansu a matsayin sarakunan Kano.