
Me magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar watau Paul Ibe ya bayyana wata aika-aika da Nafiu Bala wanda ya kaisu kotu ke shirin yi musu gobe Talata.
Yace sun samu sahihan bayanai cewa yanzu haka Nafiu Bala hana otal din Transcorp Hilton dake Abuja yana hado kan shuwagabannin jam’iyyar ADC na jihohi.
Yana so ne a gobe su masa rakiya zuwa ofishin INEC suce shine shugaban jam’iyyar na kasa na gaskiya dan INEC din ta amince dashi.
Ibe ya kara da cewa, Tuni Shuwagabannin jam’iyyar ADC na jihohin Abia da Edo suka goyi bayansa dan ya sayesu.