Tuesday, April 7
Shadow

Da Duminsa:Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya aikawa kotu da korafi kan wata Mugunta da take hakkinsa da ake masa a ofishin ICPC

Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya aikewa da kotun Magistrate dake Abuja da korafin cewa, ana kokarin take masa hakkinsa a matsayinsa na dan kasa.

ElRufai yayi zargin cewa, shugaban Hukumar ICPC din Musa Adamu Aliyu ta hannun wasu yaransa ya bayyana masa cewa sharadin sakinsa shine sai idan ya amince zai daina shiga harkar siyasa.

El-Rufai ta hannun Lauyansa yace wannan kokarine na take masa hakkinsa a matsayinsa na dan kasa wanda ba zai lamunta ba.

Zuwa yanzu dai Hukumar ta ICPC bata ce uffan ba kan zargin da malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya mata.

Karanta Wannan  Dangote ya nanata cewa, yana da man fetur din dake iya wadatar da Najeriya duk da 'yan kasuwar man sun ce ba gaskiya bane

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *