
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya bayyana cewa, da yawan rukunin gidajen da aka fara ginawa aka bari dake Abuja, ma’aikatan gwamnati ne da suka saci kudade ke ginasu.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya faru a Abuja ranar Laraba inda aka tattauna batun gidaje.
Yace da yawa ma’aikatan gwamnati ne suke fara ginin amma idan suka ajiye aiki ba zasu iya ci gaba da ginin ba.
Yace dan haka ya kafa kwamiti na musamman dan su rika bibiyar irin wadannan gidaje ana bincike wanda suka mallakesu da kuma ina suka samu kudin.