Friday, May 9
Shadow

Daga Yau Duk Wanda Kuka Gani Namiji Da Kitso Ko Dada Ku Kamashi Ku Datse Kuma Kuyi Mashi Tara….. Gwamnan Jihar Neja.

Daga Yau Duk Wanda Kuka Gani Namiji Da Kitso Ko Dada Ku Kamashi Ku Datse Kuma Kuyi Mashi Tara….. Gwamnan Jihar Neja.

Gwamnan jihar Neja Manomi Umaru Mohammed Bago ya ayyana sababbin dokoki da zasu fara aiki nan take a faɗin jihar.

Gwamnatin jihar ta Neja ta haramta bangar siyasa da duk wani abu mai kama da haka a faɗin jihar.

  1. Duk wanda aka same shi da wani makami da ya haɗa da wuka ko sanda a ɗauke shi a matsayin Ɗan fashi da makami, idan kuma yayin gardama da jami’an tsaro aka harbe shi da harsashen bindiga kada abada shi har sai ƴan uwan shi sun biya kuɗin wannan harsashen da akayi asarar shi.
  2. Duk wanda aka gani namiji da kitso ko Dada akan shi a kama shi a kuma aske kan.
  3. An Haramta amfani da Mashi mai ƙafa Biyu da mai ƙafa Ukku Keke Napepe daga ƙarfe Shidda na Yamma zuwa Shidda na Safiya.
  4. Duk wanda yazo wajen jami’an tsaro da zummar a bashi belin wani ɗan bangar siyasa shima a kama shi a kulle shi.
  5. Duk wani mai Unguwa, Dagaci ko Hakimin da aka samu yana ɓoye ƴan bangar siyasa a tsige shi kuma a kama shi.
  6. Duk wani gida da aka samu suna said kowane irin nau’in kayan maye a rushe gidan a kuma kama duk wanda aka samu a gidan.
  7. A kafa kotu ta musamman ƙarƙashin kulawar babban Alƙalin jihar da zata kula da hukunta ƴan bangar siyasa tare da tasa ƙeyar su zuwa gidan gyaran hali.
  8. Jami’an tsaro su sanya idanu sosai a wurare irin su UNGUWAR DAJI da BARKI SALE
  9. Daga yanzu OPERATION FLUSH yana ƙarƙashin Offishin Gwamnan Jihar.
  10. Duk wata mota da zata shigo babban birnin jihar Minna idan aka same ta da duk wani nau’in kayan maye a kwace ta a sanya ta cikin baitil malin gwamnatin jihar, cewar Gov. Mohammed Umaru Bago
Karanta Wannan  'Yan shi'a sun gargadi Gwwmnatin tarayya ta sakar musu mutanensu ko kuma su kai kara kotu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *