
Rahotanni sun bayyana cewa, Dalibai daga jami’ar Harvard ta kasar Amurka wadda kusan itace ta daya a Duniya kuma shuwagabannin kasar Amurkar da yawa irin su Obama can suka yi karatu sun zo matatar man fetur ta Dangote sanin makamar aiki.

An ga daliban ana kewayawa dasu inda suke shiga lungu da sako na matatar dan ganin yanda take aiki.