Thursday, December 25
Shadow

Dalibai ‘yan mata na jihar Kebbi Duk Musulmai ne, Karanta Jadawalin sunayensu

Hukumomi a jihar Kebbi sun musanta kalaman da wani ɗan majalisar Amurka ya yi cewa akwai yiwuwar ɗaliban da aka sace a jihar mabiya addinin Kirista ne.

Shugaban ƙaramar hukumar Danko/Wasagu, inda lamarin ya faru, Hon Hussaini Bena, ya tabbatar da cewa dukkanin ƴan matan da aka sace, da mai gadin makarantar da aka harbe duk Musulmai ne.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, ɗan majalisar Amurkar Riley Moore ya buƙaci magoya bayansa su taya shi yi wa ƴan matan da aka sace da mutumin da aka kashe addu’a.

A cewarsa ” duk da ba mu da cikakken bayani game da lamarin, amma mun san an kai harin ne a wani yanki da ke da kiristoci da yawa a Arewacin Najeriya, wajibi ne gwamnati ta ƙara ƙoƙari wajen kawo ƙarshen wannan zaluncin”.

Karanta Wannan  Iliyasu Muhammad ya gayyaci abokinsa gida ya kkàshèshì yayin da yake tsaka da cin Abinci a Abuja

A ranar Litinin da asuba ne wasu ƴanbindiga riƙe da muggan makamai suka shiga wata makarantar kwana da ke garin Maga a jihar Kebbi, inda suka sace ɗalibai 25, amma biyu daga cikin suka samu nasarar kuɓuta.

Ga sunayen Daliban kamar haka:

Senior Secondary School 2A:

Senior Secondary School 2B:
5. Hauwa Saleh
6. Hauwau Umar Imam

Senior Secondary School 3A & 3B:
7. Salima Garba Umar
8. Salima Sani Zimri
9. Amina G. Umar
10. Rashida Muhammad Dingu
11. Saliha Umar
12. Aisha Usman
13. Jamila Iliyasu
14. Maryam Illiyasu
15. Najaatu Abdullahi
16. Zainab Kolo

Junior Secondary School 3A:
17. Surraya Tukur
18. Hafsat Umar Yalmo
19. Maryam Usman
20. Amina Illiyasu
21. Ikilima Suleman

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda Sheikh Salihu Zariya ke cewa, idan Peter Obi ba Alheri bane, Allah ya dauki ransa kamin zabe, a gaban Peter Obin, da yawa dai sun ce dan siyasar be san abinda malam ke cewa ba

Junior Secondary School 2:
22. Khadija Nazifi
23. Hauwa’u Iliyasu
24. Hauwa’u Lawali
25. Ummu Kulsum Abdulkarim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *