Dalibar Da Ta Kammala Digiri Da Sakamako Mafi Daraja A Jami’ar Northwest Dake Kano Ta Koma Tallar Wainar Fulawa Bayan Rashin Samun Aikin Yi.

A yayin jin ta bakin Kwamared Habiba Usman Garkuwa, wadda har ta taba zama shugabar dalibai na jami’ar da ta yi, ta ce ta raba takardun neman aiki adadin da ba za ta iya tunawa ba, amma har yanzu shiru don haka ta yanke shawarar fara soya wainar fulawa da awara.
Habiba dai ta fita da sakamako mafi daraja Jami’ar Northwest a shekarar 2024 a fannin ilimin kimiyyar Biology, kamar yadda wanda ya fitar da rahoton, Abdulwahab Said Ahmad ya wallafa a Shafinsa na Facebook.