
Dan majalisar kasar Amurka, Riley Moore ya zargi tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da hannu wajan Khisan Kyiyashi da yace akewa Koristoci a Najeriya.
Moore ya bayyana hakane a matsayin martani ga Kwankwaso bayan da Kwankwason ya bayyana rashin jin dadi kan barzanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi na kawo hari Najeriya.
More yace Kwankwaso na da hannu wajan amincewa da dokar Shari’ar Musulunci wadda tasa hukuncin Khisa kan wanda yayiwa addinin Musulunci batanci.
Yunkurin shigowa Najeriya da kai hari kan wanda ta kira da cewa sunawa Kiristoci Khisan Kiyashi da Amurka tayi ya jawo cece-kuce sosai a Najeriya.