Friday, May 9
Shadow

Dan Ministan Harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar yayi magana kan Rahoton dake cewa Mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya zabgawa babansa mari

A jiyane dai muka samu rahoton dake cewa Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi,Auwal Jatau ya zabgawa ministan harkokin kasashen waje Mari.

Saidai Kakakin mataimakin gwamnan, Muslim Lawal ya fito ya musanta wannan zargi inda yake cewa ko gwamna ba zai mari Ministan ba ballantana mataimakin gwamna.

Daga baya dai hutudole ya kawo muku rahoton yanda lamarin ya faru dalla-dalla

A yau kuma Dan minista Tugga ne me suna Adam ya fito yake karin haske kan lamarin.

Adam yace rahoton dake cewa an mari babansa ba gaskiya bane.

Inda ya soki dan gwamnan jihar Bauchi, Shamsuddeen Bala Mohammed da rashin da’a na yada wannan magana wadda yace karyace.

Karanta Wannan  Kasar Nijar ta koro 'yan Najeriya 148 da suka shigar mata kasa ba bisa ka'ida ba

Yace babansa bai ce yana neman gwamnan jihar Bauchi ba amma an sakashi gaba da suka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *