
Dan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Seyi Tinubu ya bayar da tallafin Naira Miliyan 100 ga dalibai da ambaliyar ruwa da aka yi a jihar Borno a watan Satumba na shekarar data gabata ya shafa.
Dalibai daga makarantun gaba da sakandare 6 ne suka amfana da tallafin wanda ya hada da buhunan shinkafa, Taliya, Gishiri, Magi, Man Girki da sauransu.
Da yake kaddamar da rabon tallafin, Seyi Tinubu yace ya bayar da tallafinne dan karfafa gwiwar daliban su koma da ci gaba da karatu a makarantunsu.
Babban me baiwa shugaban kasar shawara akan harkar dalibai, Hon. Sunday Adebayo ne ya wakilci dan shugaban kasar inda yace gidauniyar NOELLA Foundation da Seyi Tinubu da abokansa ne suka bayar da tallafin.
Ya kara da cewa an zabi daliban ne da lamarin yafi shafa kamin raba musu tallafin.