Friday, December 5
Shadow

Dangote na son rage farashin Gas na girki saidai ‘yan kasuwar Gas din sun ce basu amince ba

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Alhaji Aliko Dangote ya bayyana shirin rage farashin Gas na girki inda yace farashin yanzun yayi tsada kuma ba lallai talaka ya iya saye ba.

Ya bayyana hakane a yayin wata ziyara da wasu masu ruwa da tsaki daga ciki da wajan Najeriya suka kaiwa matatar tasa.

Dangote yace Yana fatan ‘yan kasuwar gas din su bashi hadin kai amma idan basu bashi hadin kai ba, ba zai tsaya jiransu ba, zai koma sayarwa da mutane kaitsaye da gas din.

Dangote yace yana son har masu amfani da itace su daina su dawo amfani da gas din.

Ya kara da cewa, matatar mansa na samar da gas tan 22000 a kullun.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda wani dan majalisar Amurka ke kuka saboda Tausayin Kiristoci da ake Mhuzghunawa a Najeriya

Saidai kungiyar ‘yan kasuwar gas din ta bakin shugabansu, Godwin Okoduwa ya bayyana cewa, Dangoten yana son murkushe sune ya mayar da kasuwar Gas din tasa shi kadai.

Saidai yace ita kasuwar Gas tana bukatar hadin kai kuma sune suka kafata har ya zo ya tarar shima zai amfana dan haka bai kamata a mayar dasu saniyar ware ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *