Monday, June 2
Shadow

Dangote ya nanata cewa, yana da man fetur din dake iya wadatar da Najeriya duk da ‘yan kasuwar man sun ce ba gaskiya bane

Matatar fetur ta Dangote ta nanata cewa, tana samar da isashshen man fetur din dake iya wadatar da Najeriya.

Hakan na zuwane bayan da ‘yan kasuwa masu Depot din sayar da man fetur din suka ce sune ke wadatar da sauran sassan Najeriya dan har yanzu Matatar man ta Dangote bata iya wadatar da dukan Najeriya da man fetur din da take da dashi.

Shugaban ‘yan kasuwar, Olufemi Adewole ne ya bayyana hakan inda yace duk da yawan man fetur din da ‘yan Najeriya ke sha ya ragu, har a haka ma Matatar ta Dangote bata iya wadatar da Dukan Najeriya da mai.

Karanta Wannan  Dan kunar bakin wake da ya tayar da Bàm ya kàshe mutane 19 a jihar Borno

Yace sune ke kokarin yin hakan.

A bangare guda kuma, Wata majiya daga matatar man fetur din ta Dangote ta bayyanawa kafar Punchng cewa, Matatar tasu na wadatar da Najeriya har ma ta fitar da Man fetur din zuwa kasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *