
Dangote ya kama hanyar zama dan Afrika na farko da zai mallaki Zunzurutun kudade har dala Biliyan $30.
Rahoton jaridar Bloomberg yace Kudaden Dangote sun kari da dala Miliyan $401 a rana daya wanda shine kwatankwacin Naira Biliyan N601.
Hakan yasa yawan kudaden da ya mallaka suka karuwa zuwa Dala Biliyan 29.6.
Hakan yasa matsayin Dangote ya karu a tsakanin masu kudin Duniya inda a yanzu yake a mataki na 76