Darajar Naira ta kara faduwa a kasuwar bayan fage ta ‘yan Chanji indaka sayi dalar Amurka akan Naira 1,575 a ranar Laraba.
A ranar Talata dai an sayi dalar ne akan Naira 1,565.
Hakanan a kasuwar gwamnati ma Darajar Nairar kara kasa ta yi inda aka sayi dala akan Naira 1,586.71.
Hauhawar farashin dala dai na daya daga cikin abubuwan da ake alakantawa da hauhawar farashin kayan masarufi.
Musamman lura da cewa mafi yawan kayan amfani aana shigo dasu Najeriya ne daga kasashen waje.