
Rahotanni sun bayyana cewa, Darajar Naira ta yi rugu-rugu a kasuwar Chanji.
A wani bincike na tsanaki da aka yi, an gano cewa, Nairar ta fadi a tsakanin 14 zuwa 21 na watan Maris na shekarar 2025.
Sannan a kowane sati tana rasa darajar Akalla Naira 18.96.
A ranar Juma’ar data gabata, an kulle kasuwar Chanji Naira na da farashin N1,536.89.
Wannan a kasuwar Gwamnati kenan.
Saidai a kasuwar bayan fage, an kulle kasuwar Naira na da farashin N1,580 akan kowace dala.
Wannan bayanai duka an samosu ne daga bayanan canjin kudi daga rubun ajiyar bayanai na babban bankin Najeriya, CBN.