
Aslam Aliyu da ta fita daga ADC ta kusa da Atiku ta koma APC na ci gaba da shan suka daga wasu daga cikin yaran Atiku.
Aslam ta yi gargadin cewa idan ba’a daina sukarta kan ficewa daga APC ba, zata fasa kwai akan Atiku wanda ba zaiwa kowa dadi ba.
Saidai a martani ga wannan maganar, daya daga cikin yaran Atiku ya fito yace ya baiwa Aslam Awanni ta fito ta fasa kwan da tace akan Atiku.
Inda ya zarge ta da yawo da daya daga cikin shahararrun matasan mawakan Arewa, yace tana daukarsa zuwa kasa-kasa suna yawon shakatawa.
Ya wallafa cewa zasu bayyanawa Duniya abinda Aslam take aikatawa da mawaki Salim Smart.

Sannna ya wallafa wannan Rubutun:
Dr Aslam Mun San Abunda Kike Boyewa Duniya Akan Salim Smart Da Wasu Abubuwan, Idan Baki Fasa Kwai Ba Mu Zamu Fasa Naki Kwan, Atiku Ba Sa’an Ki Bane
Ina mai shawartar wannan matar kada ta kuskura ta bari mu shigo wannan rigimar Dan wallahi sai mun kwancē Mata Zani A Kasuwa, mun san irin abubuwan da kike boyewa duniya from A to Z in kuma kin isa yār Halak fasa kwai da kika ce zakiyi in kin fasa baki haifu ba.
Matar da shiga jahar su wahala yake bata, kullum a tsorace take, daga kasar nan sai kasar can tareda yaro ƙarami sa’an kaninta, ki zauna a Zamfaran Mana, wayanda kika koma wurin su me suka iya yiwa jahar ku a halin da kuke ciki, ki fada mana me kike dashi lokacin da kika zo gidan Atiku, kullll wallahi.
Wannan laifin ma bana kowa bane laifin Atiku ne, Shi ya fara bada kofa ake yi masa haka, yanzu da ake cin masa mūtūncī babu mai iya tsaya masa saboda duk yaran gidansa gīdādāwā ne, Atiku koda yaushe wofantār da yan jahar sa yake yaje ya kama wasu yan wata jahar wanda kullum cīn amanar sa suke.
Yanzu ka duba kwankwaso kullum akan gina yan jahar sa yake yana kara musu kwarin gwiwa shiyasa koda wasa basa bari aci mutuncīn sa, Manya manyan masu rike da median Atiku ba yan Adamawa bane, babu wani dan Adamawa dake hada kan yan media Atiku domin yi masa aiki, haka mukai ta fafutuka akan atiku amma me ya iya yi mana tunda azzālūmāī suna zagaye dashi?
Duk da mu yanzu bama tallata Atiku Amma duk wanda yace zai ci mūtūncīn Sa daga wani wajen Ko wanene sai muncī uwātār, ba’a hana kowa adawār siyasa ba amma adāwār da yakē tarē da hujja.
Atikun Jimeta