
Shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Mulkin Adalci na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yasa ‘yan jam’iyyar PDP ke ta komawa APC.
Ya bayyana hakane a Asaba, babban birnin jihar Delta yayin karbar gwamnan jihar, Sheriff Oborevwori da ya koma APC.
Ganduje yace cin zaben 2027 ya tabbata ga Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ya kuma ce akwai karin gwamnonin PDP da zasu koma APC.