Friday, December 5
Shadow

Doka ta bayar da dama idan Gwamnati ta gaza, ‘yan Najeriya zasu iya neman taimakon kasashen Duniya game da harkar tsaro>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, Doka ta bayar da dama idan Gwamnatin tarayya ta gaza, ‘yan Najeriya zasu iya neman dauki daga kasashen waje kan matsalar tsaro.

Obasanjo yace a lokacin da yayi mulki yasan cewa, Najeriya na da karfin da zata iya magance matsalar tsaro.

Yayi kira ga Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu da ta tashi tsaye ta magance matsalar dake ci gaba da ruruwa a sassa daban-daban na kasarnan.

Karanta Wannan  Najeriya ta zo ta 12 cikin kasashen Duniya mafiya talauci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *