Thursday, June 5
Shadow

Dole Sabon fafaroman da za’a zaba kada ya yi irin abinda marigayi Fafaroma Francis yayi na goyon bayan ‘yan Luwadi da Madigo, Baibul ya koya aure tsakanin namiji da mace ne kawai>>Inji Wani babban Limamin Kirista

Wani Babban maamin Kirista daga kasar Jamus, Gerhard Ludwig Müller yayi gargadin cewa sabon fafaroman da za’a zaba kada ya zama yana goyon bayan ‘yan Luwadi da Madigo.

Ya bayyana cewa duk matsin lambar da za’a masa kada ya goyi bayan wannan kazanta.

Yace Baibul ya koya musu aure tsakanin mace da namiji ne kawai inda ya yi Allah wadai da masu neman halasta auren jinsi.

Daya daga cikin abinda marigayi Fafaroma Francis yayi suna dashi shine neman baiwa ‘yan Luwadi da madigo kariya.

Karanta Wannan  Sojoji Sun Ķàma Wañi Dan Shekàŕu 55 Mai Gaŕkuwa Da Mutane A Ķano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *