
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa, dolene Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya janye kalaman barazanar da yawa Najeriya sannan ya bayar da hakuri.
Ya bayyana hakane a wajan wani taron ganawa da matasa da yayi ranar Alhamis.
Sanata Barau yace Najeriya kasa ce me cin gashin kanta dan haka ba zata bari wata kasa ta zo tana mata barazana ko katsalandan ba.
Yace ko da abinda Trump yake fada gaskiyane ba sigar da ya kamata ya biyo ba kenan, kamata yayi majalisar Dinkin Duniya ce zata shiga tsakani saboda akwai dokar kasa da kasa.
yace mu ba dabbobi bane akwai dokokin da suka tanadi hanyoyin da ake bi dan daukar mataki akan matsaloli irin wannan ba wai barazana ba.