
Kungiyar masu sana’ar tuka motocin haya, (NURTW) ta bayyana cewa, rage farashin Man fetur ba zai sa su rage farashin da suke daukar fasinja ba.
Sakataren Kungiyar na jihar Kano, Yushu’a Haruna ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da jaridar Leadership.
Ya bayyana cewa, duk da yake an rage farashin man fetur amma ba shi kadai ne suke kashe kudi wajan amfani da mitar ba, yace farashin taya ya karu hakanan farashin motar kanta ba sauka yayi ba.
Dan haka yace ba zasu rafe farashin daukar mutane ba.
Hakanan Takwaransa na kungiyar NARTO, Ado Inuwa Yakasai shima ya tabbatar da wannan magana inda yace tabbas an rage farashin man fetur amma na sauran kayan mota bai ragu ba.
Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur din daga 860 zuwa 825.