Tuesday, June 3
Shadow

Duk da doka ta bukaci hakan, Ma’aikatan Gwamnatin ciki hadda shugaban kasa, Tinubu, Kashim, da Akpabio sun ki bayyana kadarorin da suka mallaka, kuma an kasa hukuntasu

Dokar da’ar Ma’aikatan gwamnatin Najeriya, CCB ta bukaci dukun wani ne rike da mukamin siyasa ko masu hidima masa su bayyana kadarorin da suka mallaka kamin su hau mulki da kamin su saka.

Dokar kuma ta tanadi cewa dole su bayyana kadarorin da matansu ko mazansu idan macece suka mallaka da wanda ‘ya’yansu wanda basu yi aure ba suka mallaka.

Saidai da yawa basa bin wannan doka kuma an kasa hukuntasu.

Cikin wadanda basu bi wannan doka ba hadda shuwagabannin Najeriya, watau Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio.

Hakan na zuwane duk da kiraye-kirayen kungiyoyin fafutuka na neman su bayyana kadarorin nasu.

Karanta Wannan  'Yan kasar waje guda dubu daya da shida sun karbi shaidar zama 'yan Najeriya

Ookar dai ta tanadi bayyana kadarorin ne dan tsaftace aikin gwamnati da satar dukiyar Talaka da kuma hana rashawa da cin hanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *