Duk da cewa bukukuwan sallah sun wuce farashin timatir da na yaji basu sauko ba a Arewa.
Hakan kuma na faruwane duk da yake cewa, a yanzu ne sabbin wadannan kaya suka shigo kasuwa.
Bincike a jihohin Kaduna, Gombe, Nasarawa, Kogi, Adamawa, Taraba, Benue, da Sokoto ya nuna cewa maimakon farashin kayan ya sauka, kara tashi yayi sosai.
Mutane da dama sun koka kan wannan lamari.