
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyanawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cewa, duk da yawan Gwamnonin da ya tara, ba zai yi nasara ba a zaben shekarar 2027 me zuwa.
Ya bayyana hakane a wajan taron da aka yi a gidansa dake Kano.
Kwankwaso yace ba tara Gwamnoni tsaffi ko sabbi da Ministoci bane nasara, yace nasara itace a farantawa Talaka.