Kakakin majalisar Wakilai, Godswill Akpabio ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar cewa duk inda suka ga banza ta fadi ta cin abinci kyauta, kada su yi wasa da wannan damar.
Bidiyon bayanin nasa ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda ake ta bayyana mabanbanta ra’ayoyi akai.
A baya dai Akpabio ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar su rage yawan motocin da suke hawa saboda tsadar man fetur.