Thursday, June 5
Shadow

Duka kwalejojin ilimi a Najeriya za su fara ba da shaidar digiri

Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara aiwatar da sabon tsarin Dual Mandate Policy a dukkan kwalejojin ilimi na ƙasar wanda ke ƙunshe cikin sabuwar dokar kwalejojin ilimi ta 2023.

A cewar wata sanarwa daga ma’aikatar ilimi, dokar ta bai wa dukkan kwalejojin damar bayar da shaidar karatu ta digiri da kuma NCE a lokaci guda a fannin koyarwa.

Ministan Ilimi Tunji Alausa ya siffanta tsarin a matsayin “babba kuma na cigaba”.

“Wannan tsari na Dual Mandate Policy ba gyara ba ne kawai, gagarumin sauyi ne da ke bai wa kwalejojin damar bayar da shaidar NCE da kuma digiri,” in ji ministan kamar yadda sanarwar ta ruwaito.

Karanta Wannan  An kama mutane 2 da yiwa yarinya me shekaru 12 fyàd a jihar Yobe

“Tsarin zai ƙarfafa kwalejojin, ya ƙara yawan damar samun ilimi, kuma ya kyautata ingancin azuzuwan koyarwa a faɗin Najeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *