Thursday, February 26
Shadow

Emmanuel Efayeta Kuejubola ya aikawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu budaddiyar wasika inda yake neman ya bashi bashin Naira 12 zai yi kasuwanci

Wani mutum dan jihar Delta me suna Emmanuel Efayeta Kuejubola ya aikawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da budaddiyar wasika inda yake neman shugaban kasar ya bashi bashin Naira Biliyan 12.

Yace burinsa shine ya gina gidaje 400 masu dakina 2 a jiharsa ta Delta.

Yace idan aka bashi bashin, nan da watanni 36 zai mayar da kudin ya biya bashin.

Yace a baya ya taba aikawa Dangote irin wannan wasika amma bai sami amsa ba.

Yace yana fatan a wannan karin zai samu amsa daga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Karanta Wannan  Ku Daina Takalarmu, Tinubu zai iya tsige kowane gwamna, na jihar Rivers ne tsautsai ya fada kanshi ya zama na farko>>Tinubu ya gargadi Gwamnoni

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *