Wednesday, January 15
Shadow

Facebook zai kori ma’aikata dubu uku

Kamfanin Meta dake da mallakar manhajojin Facebook, Thread, Instagram da WhatsApp na shirin korar ma’aikata 3600 daga aiki

Za’a kori ma’aikatan aiki ne saboda rashin kwazo inda za’a maye gurbinsu da wasu kamar yanda kafar Bloomberg ta ruwaito.

Wadannan ma’aikatan na wakiltar kaso 5 na kafatanin ma’aikatan kamfanin na Meta.

Kamfanin dai na da jimullar ma’aikata 72,400.

Shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg ya bayyana cewa ya yanke shawarar mayar da hankali kan kwazon ma’aikata.

Karanta Wannan  Hotuna: Dandazon Jama’a Sun Halarci Zaman Fadan Sarki Aminu Ado A Yau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *