
Babban Limamin Kirista, Fafaroma Francis ya nemi a yi sulhu a yakin da ake tsakanin kungiyar Hamas da Israela.
Yayi wannan kirane a yayin da ake bukukuwan Easter.
Yawan wanda aka kashe a Falasdin ya haura mutane dubu 50 ciki hadda mata da kananan yara.
Fafaroma ya kuma bayyana a karin farko tun bayan da yayi doguwar rashin lafiya a bainar jama’a.
Hakanan Mataimakin shugaban kasar Amurka, J.D Vance ya halarci fadar Fafaroman yayin da ake bukukuwan Easter.