
Rahotanni sun bayyana cewa, alkaluman farashin kayan abinci ya sauka a Najeriya inda a yanzu yake a maki 18.02 a watan Satumba daya gabata.
Idan aka kwatanta da watan Augusta daya gabata, Alkaluman na matsayin maki 20.12 wanda hakan ke tabbatar da an samu sauki sosai.
Hukumar kula da kididdiga ta kasa, NBS ce ta bayyana hakan a sanarwar data fitar ranar Laraba. Rabon da makin na NBS ya sakko kasa da 20, shekaru 3 kenan.