Monday, May 26
Shadow

Farashin kayan masarufi sun yi sauki a Najeriya

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga kashi 24.23 a watan Maris ɗin 2025 zuwa kashi 23.71 a watan Afrilun 2025.

Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta ce hauhawar farashin da aka samu a watan Afriliu ya nuna an samu ragin kaso 0.52 na hauhawar idan aka kwatanta da watan Maris.

“Wannan na nuni da cewa hauhawar farashin Ta shekara-shekara Ta ragu a watan Afrilun 2025 idan aka kwatanta da watan Afrilun 2024.”

Dangane kuma da hauhawar farashin kayan abinci a watan Afrilun 2025 ta kasance kaso 21.26 kamar yadda ke faruwa a shekara-shekara.

Karanta Wannan  Tashin bàm ya kàshè mutum 26 a jihar Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *