Wata hukumar dake saka ido akan farashin kudaden Duniya, Fitch Ratings ta yi hasashen cewa, farashin Naira zai kare akan 1,450 ne akan kowace dala har zuwa karshen shekarar 2024.
Daraktan hukumar, Gaimin Nonyane ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi kan Najeriya da kasar Misra/Egypt.
Ya kara da cewa, har yanzu Naira bata daidaita ba akan farashi daya tun bayan da aka cire tallafin dala.
Yace zuwa shekara me zuwa ma Nairar zata ci gaba da faduwa amma ba zasu iya bayyana a farashin da zata tsaya ba.