Tuesday, September 1
Shadow

Mutane na cikin wahala da Yunwa a Najeriya>>Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, mutane na cikin wahala da yunwa a Najeriya.

Ya bayyana hakane a legas wajan wani taro da aka gayyaceshi.

Obasanjo yace matsalar tsaro ce ta daidaita kasarnan sannan ya koka da matsalar rashin shugabanci na gari.

Yayi kira ga shuwagabannin kasar da su tashi tsaye wajan inganta rayuwar mutane.

Yace akwai bukatar canja Shuwagabanni wanda zasu kawo ci gaba irin wanda ake bukata.

Karanta Wannan  Faduwar da Tinubu yayi zata iya faruwa akan kowa, Cewar Sheikh Pantami, saidai da yawa sun sokeshi akan bai ce komai ba kan kashe-kashen da ake a Arewa amma gashi yana kare shugaban kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *