Friday, December 5
Shadow

Filaye Hectares 30 ne Wike ya kwacewa sojoji a Abuja, Ji karin bayani

Rahotanni sun bayyana cewa, Filaye Hectares 30 ne aka baiwa manyan sojoji masu ci da wadanda suka yi Ritaya ministan babban birnin tarayya, Abuje Nyesom Wike ya kwace.

Rahoton Sahara reporters yace Wike bayan kwace filayen ya rabawa abokai da na kusa dashi su .

Saidai filin da suka yi rikici da Soja Yerima akai, Wike yayi rikici da soja me filin inda suka ce masa ya je kotu kamar yanda yakan gayawa mutane idan ya kwace musu fili.

Amma saboda yasan bashi da gaskiya, Bai je kotun ba.

Shine ya kwashi jami’an tsaro kusan 50 da motocin rushe gini ya nufi filin dan kwace shi amma ya hadu da Turjiya daga wajan soja Yerima.

Karanta Wannan  Karya ministan Lafiya yake, bamu janye yajin aiki ba>>Inji Kungiyar malaman Jinya(Nurse) na Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *