Friday, December 26
Shadow

Ganduje ya dawo daga London bayan ya shafe wata domin neman lafiya

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya dawo Najeriya daga Landan a jiya Laraba.

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya tafi ƙasar Birtaniya domin neman magani jim kaɗan bayan murabus ɗinsa daga shuagabancin jam’iyya mai mulki a ƙasar.

Da ya ke tabbatar da wannan batu ga jaridar The PUNCH, tsohon shugaban ma’aikatansa, Mohammed Garba, ya ce Ganduje ya sauka a Nijeriya ne a safiyar jiya Laraba bayan shafe kusan wata guda a waje.

“Eh, ya dawo Najeriya yau. Ya dawo cikin koshin lafiya, kuma ya ƙarasa gidansa,” in ji Garba, yayin da ya ke tabbatar wa da jaridar PUNCH.

Ya ƙara da cewa Ganduje ya bar Najeriya zuwa Landan ne kwana biyar bayan ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar domin neman lafiya.

Karanta Wannan  Ƴan Najeriya miliyan 31 na fuskantar matsalar ƙarancin abinci - MDD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *