Ana amfani da Ganyen Gwaiba wajan magance matsaloli daban-daban na jikin dan Adam.
Kuma infection musamman na gaban mata na daya daga cikin abubuwan da ake amfani da ganyen gwaiba wajan magance su.
Saidai amfani da ganyen gwaiba wajan magance infection na mata a gargajiyance ne kadai ake hakan kuma ana yi ne ta hanyar dakashi ko markadashi a shafa a gaban macen.
Hakanan a wani kaulin ana amfani dashi wajan magance kaikayin gaba na mata, shima ba turawa ake yi cikin gaban ba, shafawa ake yi.
Saidai duka wannan a kimiyyar lafiya ba’a tabbatar dashi ba amma kuma ba’a bayyana wata illa da amfani da ganyen gwaban ke da ita ba wajan magance infection.
Ma’ana mutum zai iya gwadawa da neman dacewa, saidai a bi a hankali kada a yawaita amfani da ganyen kwaban saboda duk kyawun abu idan aka wuce gona da iri, yana iya komawa ya zama illa.
Sauran magungunan da ganyen Gwaba yake yi sun hada da:
Maganin Atini ko zawo ko gudawa: Yana taimakawa sosai wajan magance ciwon cikin da ake ji yayin zawo, atini ko gudawa idan aka sha ganyen gwaiba.
Ciwon Lokacin Al’ada: Ganyen Gwaiba na taimakawa wajan magance matsalar ciwon lokacin al’ada.
Ciwon Dasashin Hakora: Ga wadanda ke fama da ciwon dasashin hakora zasu iya jaraba kuskure baki da ruwan ganyen gwaiba.
Maganin Hawan Jini: Bincike ya tabbatar da cin gwaba da yawa a rana na tsawon makonni 12 yana taimakawa sosai wajan magance matsalar hawan jini.
Ciwon Gwiwa: Bincike ya nuna cewa mutane dake fama da ciwon gwiwa idan suna shan ruwan ganyen gwaba yana taimakawa sosai wajan magance matsalar.
Ganyen Gwaba na kuma maganin:
Ciwon Sugar.
Tari.
Amai.
Rage kiba.
Yana taimakawa wajan kara tsawon gashi.
Yana taimakawa wajan samun isashshen Bacci.
Yana maganin ciwukan Fata.
Da dai Sauransu.