
Gawuna ya sa wayarsa a ‘DND’ yayin da Tinubu ke kokarin dakile komawarsa Kwankwasiyya
Rahotanni daga fagen siyasar Jihar Kano sun nuna cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya zama wanda nema ruwa a jallo, yayin da wayarsa ta kasa samuwa a daidai lokacin da ake rade-radin shirin ficewarsa daga jam’iyyar zuwa Kwankwasiyya daga nan kuma zuwa ADC.
Ana zargin cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci wasu manyan jiga-jigan APC da su dakatar da yunkurin Gawuna na sauya sheka zuwa tafiyar Kwankwasiyya ko kuma jam’iyyar ADC.
Daily Nigerian, ta rawaito cewa Gawuna na shirin hada kai da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin kifar da Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaben 2027 mai zuwa.
Majiyoyi sun bayyana cewa an shafe lokaci an kasa samun Gawuna ta waya, lamarin da ya kara janyo rade-radi kan cewa yana gudanar da wasu muhimman tuntubar siyasa a wajen kasar.
Rahotanni sun ce ya fara tafiya Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah, kafin daga bisani ya wuce wata kasa a yankin Arewacin Afirka domin hutu.
Wasu majiyoyi sun kara da cewa Gawuna ya sanya wayarsa a “Do Not Disturb” domin kaucewa matsin lamba daga shugabannin jam’iyya da ke kokarin hana shi ficewa daga APC.
Ana kuma zargin cewa wannan ci gaba ya jefa APC cikin rudani a Kano, inda ake cewa an tura wasu manyan ‘yan siyasa domin shawo kan Gawuna ya ci gaba da zama a jam’iyyar, tare da yi masa tayin tikitin Sanatan Kano ta Tsakiya kai tsaye a zaben 2027.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa sauya shekarsa zuwa bangaren Kwankwasiyya na iya sauya akalar siyasar Kano baki daya, musamman la’akari da irin goyon bayan da yake da shi a tsakanin matasa, malamai da ‘yan kasuwa.
A gefe guda kuma, magoya bayan Gawuna na ci gaba da nuna damuwa kan abin da suka bayyana a matsayin wulakanta shi a cikin APC, da kuma rashin ba shi muhimman mukamai tun bayan kayen da ya sha a zaben 2023.
Haka zalika, akwai korafe-korafe kan rashin biyan wasu hakkokinsa a matsayinsa na tsohon mataimakin gwamnan jihar.