Tuesday, January 7
Shadow

Giya ce dalili na 3 na kamuwa da cutar daji(cancer)

Babban masanin kiwon lafiya na kasar Amurka ya bayar da shawarar cewa kamata yayi ace duk giyar a ake sayarwa a kasar a saka mata gargadi na cewa shanta zai iya kai mutum ga kamuwa da cutar daji(Cancer), kamar dai yanda gargadin yake a jikin kwalayen taba.

Vivek Murthy’s ya bayyana cewa shan giya na cike da hadarin kamuwa da cutar Daji(Cancer) akalla kala bakwai ciki hadda Cancer nono data hanji da sauransu.

Yace bayan yawan kiba da taba sigari, Shan giya shine abu na 3 da za’a iya hakura dashi dan kaucewa kamuwa da cutar daji.

Rahoton na jaridar New York Post yace shan giya na sanadin kamuwar mutane akalla dubu dari da cutar Cancer wanda kuma take sanadiyyar kisan mutane akalla dubu ashirin duk shekara.

Karanta Wannan  Magidanci ya yi karyar cewa an yi garkuwa dashi bayan da ya ranci kudi Naira Miliya 1 ya buga caca dasu aka cinye kudin

Wannan adadi yafi mace-macen da ake samu sanadiyyar hadarin mota.

Masu shan giya na cikin hadarin kamuwa da cancer makogoro, data baki, data Anta, da ta murya data nono da sauransu.

Yayi kiran a kara wayarwa da mutane kai kan lamarin tare da yada illar da shan giya ke da kwai ga lafiyar dan Adam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *