Tuesday, June 3
Shadow

Goodluck Jonathan, da Bukola Saraki sun yiwa Tsohon Shugaban kasa, Marigayi Umar Musa ‘Yaradua addu’a

A yayin da tsohon shugaban kasa, Marigayi, Umar Musa ‘Yaradua ya cika shekaru 15 da rasuwa, Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya masa addu’a.

Yace ‘yaradua ya sashi ya kara fahimtar aikin gwamnati da kyau.

Yace bai cika yawan magana ba, kuma idan yayi magana babu siyasa a ciki zaka ji ta me ma’ana ce.

Yace bashi da girman kai, yana da kankan da kai.

Inda a karshe yayi mai fatan Allah ya ci gaba da sakashi ciki mutane na gari a Aljannah Firdausi.

Shima Bukola Saraki a nasa sakon cewa yayi, Muna girmama tsohon shugaban mu da bashi da girman kai ga hangen nesa .

Karanta Wannan  Dakatarwar da Shugaba Tinubu yawa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara na Tangal-Tangal yana ta neman 'yan Majalisa su amince masa domin idan basu amince ba dole ya janye dakatarwar

Yace manyan abubuwan da ake tuna tsohon shugaban kasar dasu sune, hadin Kan Najeriya, Sulhu da ‘yan Naija Delta, zaman lafiya da gyaran Zabe.

Yayi fatan Allah ya ci gaba da yi masa Rahama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *