Sunday, December 22
Shadow

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya tsere ana saura kwanaki 2 ya mika mulki saboda tsoron kamun EFCC

Rahotanni sun nuna cewa,gwamnan jihar Edo me barin Gado Godwin Obaseki ya tsere daga jiharsa saboda tsoron kamun EFCC.

Gwamna me jiran gado, Senator Monday Okpebholo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta bakin kakakinsa, Godspower Inegbe.

Yace Gwamna Obaseki yayi amfani da motar bas ne yayi basaja ya tsere daga jihar.

Yace ikirarin gwamnan na cewa shi me mutanene karyace inda ba haka ba bai kamata yayi amfani da bas ys tsere daga jihar ba.

A baya dai an ji gwamna Obaseki na fadin cewa yasan hukumar yaki da rashawa da cin hanci EFCC na shirin kamashi bayan ya sauka daga kan mulki amma baya jin tsoro.

Karanta Wannan  Hukumar shari'a ta hukunta ma'aikatanta takwas a jihar Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *