
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aikewa da majalisar jihar kudirin dokar haramta Madigo da Luwadi.
Gwamnan ya aike da kudirin dokar ne dan tabbatar an haramta wannan bakar dabi’a sannan an hukunta duk wanda aka kama na yin hakan.
A lokutan baya an rika samu rahotannin auren jinsi a jihar ta Kano.