Gwamnan jihar Naija, Muhammad Bago ya bayar da shawarar a rika amfani da yaren Hausa wajan koyar da dalibai a makarantun Firamare da Sakandare a jihohin Arewacin Najeriya.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka yi a Minna ranar Talata inda yace daukar wannan mataki zai kara karfafawa yara shiga makaranta.
Yace kamata yayi a rika Amfani da Turanci a matsayin Subject kawai amma ba yaren koyar da karatun ba.
Gwamnan ya jawo hankalin Gwamnonin Arewa dasu canja tsarin karatun yankin dan karfafa gwiwar yara su shiga makaranta.